Labaran Kano
Hukumar tace fina-finai ta kasa ta kone fina-finan batsa a Kano
Hukumar tace fina-finai ta kasa ta yi kira da ‘yan kasuwa da kamfanonin shirya fina finai dasu mai da hankali wajen inganta harkokin saida fina finai masu mahimmanci da ma’ana a cikin alumma.
Shugaban hukumar mai kula da shiyyar Kano Alhaji Umar Fagge ne ya bayyana haka lokacin da suke kona fina-finai na basa a harabar hukumar dake nan kano.
Ya kara da cewa sun kama fina-finai batsa guda dubu biyar a kasuwanin jihar nan domin karkabe bata gari a cikin kasuwanin.
A nasa jawabin hakimin karamar hukumar Dala Alhaji Abdullahi Lamido Sunusi Turakin Kano ya ce, dole ne iyayen yara su sa ido sosai a irin fina- finai da yaransu suke kallo domin wasu fina-finai suna bata tarbiyar yara.
Wakilin mu Shamsu Da’u Abdullahi ya rawaito cewa shuwagabannin kamfanonin shirya fina-finai da mayan jami’an tsaro sun hallaci kona fina -finai na basa guda dubu biyar.