Connect with us

Labaran Kano

Gwamnatin tarayya za ta samar da wuta mai amfani da hasken rana

Published

on

Ministan wutar lantarki na kasa Injiniya Sale Mamman, ya ce akwai bukatar samar da karin manyan dama -damai da za su kara inganta harkar samar da wutar lantarki a kasar nan.

Injiniya Sale Mamman na bayyana hakan ne yayin zantawar sa da gidan radiyo freedom kan cika shekaru dari da yayi a ofis na irin ayyukan da ya gabatar a ma’aikatar.

Ya ce ana sa ran samun wutar lantarki mega watt dari bakwai a tafkin Shiroro da na kainji, wanda a yanzu da kyar ake iya samar da mega watt dari hudu, hakan na daya daga cikin kalubalen da ke kawo koma baya a sha’anin wutar lantarki a kasar nan.

Ya kuma ce ma’aikatar wutar lantarki sun dukufa wajen ganin ta ci gaba da samar da wutar lantarki yadda ya kamata musamman ta hanyar hasken rana da iska.

Sale Mamman ya kuma ce duba da rashin ishashiyar wutar lantarki da ake samu a Arewacin kasar nan ne ya sanya ma’aikatar za ta samar da Karin tashohin wutar a nan Arewa musamman a jihar Kano dan inganta masana’antun dake yankunan.

Injiniya Sale Mamman ayayin tattaunawar ya kuma ce, manyan kamfanonin dake karbar wutar dan rabawa ga al’umma suna daya daga cikin wadanda ke kara ta’azzara rashin wuta a kasar nan ta yadda idan an turo wutar basa iya karba dan rabata ga jama’a.

Ya kuma ce kamfanonin dake raba wutar a kasar nan sunfi so sukai ta zuwa unguwannin da suke biyan su kudade masu Asoka ko kuma kamfanoni, ta yadda ta hakan ne kadai suke iya samun kudade masu yawa.

Injiniyya Sale Mamman ya ce jihohi da dama a kasar nan da dama basa iya biyan kudin wutar da suka karba, inda ya buga misali da jihar Lagos da cewa bata iya biyan kashi daya cikin hudu na kudin wutar da ake bata a duk wata.

Shugaban ya ce hanya da ya ce za’a iya bi dan magance matsalar rashin samun ishashiyar wutar lantarki ,ita ce samar da mitoci a gidaje ta yadda kowa zai iya sanin wutar da yake sha, suma masu kamfanonin su samu saukin karbar kudaden wutar a hannun al’umma.

Inda ya ce ma’aikatar ta na nan ta na gudanar da tsari ta yadda za ta sanyawa kowanne gida da shaguna da kamfanoni mita yadda kowa zai dinga sanin wutar da yake sha kuma za’a sanya mitocin ba ko sisin mutun ta yadda za’a dinga cire kudin mitar ahankali har mutun ya gama biya.

Ya ce yanzu ma’aikatar na nan na duba yiwuwar samun masalaha tsakanin masu karbar wuta da masu rabata yadda za’a samu ingantacciyar wuta musamman yadda za’a cigaba da samun cigaban tattalin arzikin da ya kamata.

Injiniyya Sale Mamman ya ce ma’aikatar na nan na kokarin shigo da tsarin da zai baiwa kananan ‘yan kasuwa wutar lantarki suna sayar da ita ga al’umma ta yadda wadanda ke bukatar wutar da yawa za su dinga samunta yadda ya kamata dan saukaka musu aiyuukan su da cigaban tattalin arzikin su.

Ko da aka tambaya shi wasu kasashen da ke makwabtan da kasar nan ke samun wuta awanni ashirin da hudu batare da daukewa ba kuma suna samun wutar ne daga nan Najeriya sai ya ce kasashen na biyan kasar nan kudin wuta yadda ya kamata sabanin yadda abin yake a nan gida Najeriya.

 

Coronavirus

‘Yan kasuwa sun nemi Ganduje ya bude Kasuwanni sau biyu a mako

Published

on

‘Yan Kasuwa sun  bukaci gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, da ya duba dokar kulle na zaman gida tare da bada dama ga ‘yan Kasuwannin Sabongari da Kwari da na  Singer domin fitowa Kasuwancin su a kebabbun ranakun  da aka ware a mako don gudanar da nasu Kasuwancin.

Alhaji Imamu Tafida, Tafidan Dakayyawa kuma daya daga cikin Dattijan Kasuwar Muhammad Abubakar Rimi, wato Sabongari shi ne yayi wannan kira duba da mawuyacin halin da ‘yan Kasuwan suke ciki kamar yadda jagororin  Kasuwar suka tabbatar.

Alhaji Imamu Tafida, ya ce ‘yan kasuwa da dama, sun tafka asara ta miliyoyin nairori sakamakon rufe kasuwannin, kasancewar kayan da suka siyo basu shigo ba dalilin hana shige da fice, hakazalika wanda ake dasu a kasuwar ba a siyar dasu ba.

Tafidan Dakayyawan, ya kuma bada tabbaci ga gwamnati na cewar zasu yi duk mai yiwuwa wajen daukar matakan kariya daga cutar ta Corona daga bangaren su da masu mu’amala dasu da zarar an basu damar gudanar da Kasuwancin su.

Wakilin mu, Aminu Halilu Tudunwada, ya ruwaito mana cewa, Alhaji Imamu Tafida, ya bukaci al’umma dasu bi umarnin hukumomi da ma’aikatan lafiya, tare da rubanya addu’a domin ganin an kawar da wannan annoba da ta kawo tsaiko a al’amuran yau da kullum na jama’a.

Continue Reading

Coronavirus

Amsoshin tambayoyi 20 kan cutar Corona – Dr. Ibrahim Musa

Published

on

Wadannan wasu ne daga amsoshin tambayoyin ku da likitan mu Dakta Ibrahim Musa na asibitin koyawarwa na Malam Aminu Kano ya amsa muku ta shafin mu na Facebook wato Freedom Radio Nigeria.

 1. Tambaya ta farko:

Sani Mai Rodi

Wai Dan Allah Mai yasa ba a Nuna Mana masu cutar Coronavirus a fili Dan Al’umma su kara tabbatar da akwai ciwon.

Ibrahim Musa
Akwai confidentiality na marar lafiya.

Mus’ab Ibrahim Sulaiman

Amma Mai Coronar Nigeria kadai keda confidentiality ko, tunda muna ganin na sauran kasashe

Ibrahim Musa

Idan mara lafiya ya bada izni ‘yan jaridu za su iya daukar hotonsa.

Wannan aikin yan jaridu ne bana hukumar lafiya ba, Wanda ya fara kamuwa da ita a Kano anyi ta yamididi da sunansa ana bata shi.

Wannan yasa saboda kiyaye hakkinsu ba a fada sai ga wanda ya zama a hakku.

 

 1. Tambaya ta biyu:

Sagir Umar Sheka

Ina muku fatan alkhairi tambayata ita ce zuwa yaushe suke sa ran zasu shawo kan wannan cutar corona

Ibrahim Musa 
Anci karfin ciwon sosai, Insha Allah nan bada dadewa ba za’a shawo kan ciwon.

 

 1. Tambaya ta uku:

Muhammad S Muhammad

Aslm Dakta Wanda yake da Covid-19 Bayan mutum ya kamu da ita idan ya warke ya rabu da ita baki daya ne ko kuma akwai wasu illoli da take yiwa mutum a jiki?.

Ibrahim Musa
Tunda sabon ciwo ne, ba za a iya sanin ko akwai wasu matsaloli ba sai nan gaba. Wadansu sukan samu stroke saboda ciwon wanda ko mutum ya warke zai fama dashi zuwa wani lokaci.

 

 1. Tambaya ta hudu:

Abdulganiyu Isah Wagini

Aslm Dakta tambayata anan ita ce,
Ta wanne irin hanyoyi zakayi mu’amala da wanda ya kamu da korona kuma ya warke, sannan kuma wacce hanya al’umma zasu bi domin dakile cutar nan ba tare da ta ci gaba da yaduwa ba a cikin al’umma, Nagode a tashi lafiya.

Ibrahim Musa 
Idan ya warke sai a cigaba da mu’amala babu matsala.

Amma a kula da tsaftar hannu, tsaftar jiki da tsaftar muhalli.

A rika bada tazara ta taku shida idan an shiga taro.

A saka Facemask duk lokacin da ake waje.

Banda musabiha ko saka hannu ana dakuma fuska.

Idan mutum yaji bashi da lafiya, ya killace kansa har sai an gano mai ke damunsa anyi masa magani ya warke, Shine za a iya dakile yaduwar ciwon.

 

 1. Tambaya ta biyar:

AbdulJabbar Musa 

Salam Dakta Tambayata itace: “ko akwai wata na’ura da jami’an lafiya zasu yi amfani da ita wajen gwajin kwayar cutar CORONA wadda zata nuna sakamakon nan take kamar yadda Infrared Thermometer take nunawa?.
Sannan kuma meyasa jami’an tsaro na bakin border ba’a basu kayan aiki (personal protective equipment) kamar yadda na lafiya suke samu?”

Ibrahim Musa

Akwai na’urar dake nuna ciwon cikin minti 15, amma ba a Nigeria ba.

Ba mamaki nan gaba a kawo ta tunda bata dade da fitowa ba.

PPE suna ne mai fadi, Maaikatan border idan suka saka facemask da gloves sun isa.

A asibitin ma su ake sawa sai kalilan dake duba masu COVID-19 dake saka full protective gear. Ita full gear tana da zafi wanda a awa daya mutum na iya gumi da yakai litre guda.

 

 1. Tambaya ta shida:

Murtala Yahaya Musa Sarauta 

Assalamu alaikum,
Muryar jama a Allah ya taimakeku.
Tambayata Itace Idan na kasa samun lambar masu zuwa sudauki wanda yake da alamomin wannan cutar me yakamata nayi domin dakile cutar da kuma ni na samu sauki kafin Allah yasa na same su a waya.

Ibrahim Musa
Killace kai. Cin abinci mai gina jiki. Shan ruwa sosai. Tsaftar hannu da ta jiki. Yawan shan kayan marmari da yayan itatuwa.

Idan kaji kamar ciwon zai galabaitar da kai kaje asibiti ka sanar dasu halin da kake ciki.

 

 1. Tambaya ta bakwai:

Ilyasu Bin Galadimawa 

Slm fatan alkhairi a gareku ina yiwa babban bako barka da zuwa tambaya ta itace ta yaya mutun zai san ya kamu da wannan cutar sannan kuma ta yaya zai sanar daku Allah ya maida bako gida lfy.

Ibrahim Musa 
Alamomin ciwon sun hada da zazzabi, tari mara kaki, shakewa ko daukewar numfashi, gudawa, ciwon jiki, rashin jin kamshi ko dandano. Idan kana jin daya ko duka alamomin sai ka kira lambar State Rapid Response ta jiharka suzo suyi maka gwaji a tabbatar ko kana da ciwon.

 

 1. Tambaya ta takwas:

Baban Humaira Rimin Kebe

Tambaya ta anan shine don Allah Freedom ance a zauna a gida amma har yanzu kullum ana samun karin mutane a nan jihar Kano to yanzu haka za a yi ta tafiya?

Ibrahim Musa 
Zaman gida yana rage yaduwar ciwon ne amma tunda ba kowa ne ke zaman gidan ba har yanzu ana samun mutane suna hada-hada da cakuduwa.

Wannan yasa ciwon yake cigaba amma ba kamar yadda da an bar kowa yayi abinda ya ga dama ba.

 

 1. Tambaya ta tara:

Sulaiman Gambo Idris

SLM ya maganar maganin da aka karbo daga Madagascar yaushe za a fara amfani dashi a nan Nigeria kuma ina kira da likitoncin mu suma yakamata suyi hobbasa su samar da maganin wannan cuta.

Ibrahim Musa 
Maganin Madagascar na gargajiya ne. Shugaban kasa yace ayi bincike a tabbatar da menene shi tukun kafin ya a cewa jama’a suyi amfani dashi.
Likitocin Nigeria suna iya kokarin su. Bincike irin wannan yana bukatar kudi da kayan gwaje-gwaje.

 

 1. Tambaya ta goma:

Jameelah T Rabiu

Tambayoyi na Dakta su ne, Wanda ya kamu ya warke yana iya kuma kamuwa? a wani qaulin ance bata kama yara, ya abin yake? idan mutum yaji alamu a jikinsa ba tare da an gwadashi ba, me ya kamata yayi?

Ibrahim Musa 

Tambaya ta daya na amsa ta a sama. Ta biyu amsar itace tana kama yara sai dai bata cika tsanani a jikinsu ba.

Idan mutum yaji alamun corona sai ya killace kansa, ya kuma kira ayi masa gwaji.

 

 1. Tambaya ta goma sha daya:

Abubakar Fulani Goron Dutse 

Slm, ya aiki Allah ya taimaka yayi jagora, shin wai dagaske ne ace coronavirus ta kusa yin experience, kuma da gaske ke Nigeria tana daga cikin kasashen da suka Nemo maganin ta?

Ibrahim Musa 
Kana nufin expiry? Har yanzu dai ana fama da ciwon. Amma abubuwa na dada lafawa a hankali.

Nigeria tana nata kokarin. Amma har yanzu dai ba’a samu wani magani Dan Nigeria ba.

 

 1. Tambaya ta goma sha biyu:

Auwal Shuaibu Amfani

Fatan alkhairi ga wannan tasha mai farin jini kuma ina yiwa masu gabatar da wannan shirin barka da shigowa studio, tambayata ita ce mai cutar covid-19 zai iya warkewa daga cutar gaba daya kuma cutar ta kara kamashi a karo na biyu 2.

Ibrahim Musa 

An samu wasu gwaji ya nuna sun kamu da Corona bayan warkewa.

Amma daga baya anyi tunanin ko ragowar matattun RNA na virus dinne ba wai sabon ciwo bane.

 

 1. Tambaya ta goma sha uku:

Uban Salo 
Tambayata ita ce wai shin coronavirus a ina ake killace al’umma wadanda suka kamu da ita, kuma sai naga ban taba jin wanda akace min gashi wani dan uwansa ya kamu da ita menene sirrin lamarin ne?

Ibrahim Musa

Ana killace wadanda suka kamu da ita ne a asibitocin da gwamnati da ware da sunan isolation centers.

A Kano sun hada da asibitin Kwanar Dawaki da kuma Muhammad Buhari Specialists Hospital dake Giginyu.
Mutane da yawa ‘yan uwansu ko iyayensu ko abokansu sun kamu da ita. Wasu ma ita ta jawo ajalinsu. Ba mamaki baka taba ganin wanda ya kamu HIV ba. Amma hakan baya nufin babu HIV.

 

 1. Tambaya ta goma sha hudu:

Aremeenu Ubalee Gaya 

Assalamu alaikum ina yiwa babban likita barka da zuwa tambayata itace ance har yanzu ba’a kai ga gano maganin corona virus ba amma kuwa munji ana warke to wai tayaya ake warkewa daga wannan cuta.

Ibrahim Musa
Da yawa garkuwar jikin Dan Adam ce take yakar cutar. Wadansu da ake kwantarwa ana basu kulawa da tallafi har sai garkuwar jikinsu tayi tasiri ta murkushe ciwon.

 

 1. Tambaya ta sha biyar:

Aminu Abubakar 

Assalamu alaikum kowa ya yarda akwai corona amma abun tambaya shine me yasa ba a nuna mana marasa lafiyar?, me yasa bama ganin video lokacin da ake basu kulawa me yasa bamu taba ganin wanda yace an dauki dan uwansa ko dan unguwarsu mai cutar ba?, saidai kullum muji cewa an samu mutun kaza bamu gamsuba, bamu san su ba, kuma muna da abokai a kowace unguwa acikin garin nan.

Ibrahim Musa
Saboda mara lafiya nada sirri da bai kamata a tozarta shi ba sai dai idan shi ne da kansa ya fadawa alumma.

 

 1. Tambaya ta sha shida:

Usman Mukhtar Muhammad 
Tambayata a nan shine wai wani irin magani kasar China tayi amfani dashi da ta samu lagon cutar covid-19 sosai?.

Ibrahim Musa

Babban maganin da tayi amafani dashi shine yin gwaji, killace wadanda ke da ciwon domin basu kulawa ta musamman, da kuma zakulo wadanda mai ciwon yayi mu’amala dasu a gwada su a gano suwa suka kamu.

Sannan kasar ta kulle garin Wuhan har sai da aka ga Corona ta daina yaduwa a tsakanin alumma.

 

 1. Tambaya ta sha bakwai:

Abbakar Sadeeq Abbakar 

Slm ina yiwa babban bako barka da zuwa tambayata a nan guda daya ce, wai shin wadanda ake samu da corona mai yasa ba a fadar sunan su da kuma local govenment dinsu?.

Ibrahim Musa
Saboda kowanne mara lafiya yana da ‘yancin a sirrinta abinda ya shafe shi. Ana kiran abin da confidentiality.

 

 1. Tambaya ta sha takwas:

Yusif Abban Anisah Karwai 

Slm zan iya kamuwa da corona idan nayi amfani da dardumar wanda yake dauke da ita?

Ibrahim Musa
Yana iya yiwuwa amma bashi ne hanyar da tafi yaduwa ba.

 

 1. Tambaya ta sha tara:
  Usman Lawal

Wai wadanda ake samu sun warke daga cutar wane irin magani ne suke sha domin mu tanada.

Ibrahim Musa
Ana basu tallafi kalakala. Kowanne magani sai likita yaga dacewar sa kafin ya bayar.

 

 1. Tambaya ta ashirin:

Abdulkabeer Muhammad Jamiu

Ina da tambayoyi guda biyu kamar haka:

(1) shin sauro zai iya yada cutar korona?

(2) Jariri da mai dauke da cutar corona ta haifa, shin zai iya daukar cutar?

Ibrahim Musa 

Sauro baya yadata. Akwai yiwuwar jariri ya iya dauka.

Amma yawancin yara basa samun ciwo mai tsanani.

Continue Reading

Coronavirus

Covid-19: Babu hawan sallah a Kano

Published

on

Maimartaba Sarkin Alhaji Aminu Ado Bayero yayi kira ga al’ummar Kano da su kiyaye dangane da yanayin da ake ciki na annobar Covid-19 da ta janyo sauyawar al’adun fada.

Sarkin ya bayyana hakanne a daren Asabar a Kofar Kwaru yayin da yake jawabi a gaban manyan hakiman sa kan yadda za a gudanar da sallar bana.

Maimartaba Aminu Ado ya ce babu hawan sallah na al’ada da masarautar Kano ta sabayi duk shekara saboda yanayin Corona.

Sarkin ya kara da cewa maimakon hakan Sarki zai tafi idi a kafa, inda zai fito ta kofar Fatalwa har zuwa filin idi na Kofar Mata da safe.

Bayan an idar da sallar idi kuma Sarkin zai biyo ta unguwar Kofar Wambai da Zage, sannan ya biyo ta Dorayi da Shahuci daga nan ya zarto zuwa Kofar Kwaru a Mota.

Ana sa ran Sarkin zai yi jawabi ga al’ummar Kano bayan sakkowa daga sallar idin a Kofar Kwarun kamar yadda al’adar masarautar Kano take.

Wakilinmu na fadar sarkin Kano Muhammad Harisu Kofar Nassarawa ya rawaito mana cewa Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya jajantawa al’ummar Kano sakamakon rashe-rashen da aka samu sannan yayi fatan marasa lafiya Allah ya basu lafiya.

A karshe Sarkin yayi kira ga al’ummar Kano da su cigaba da kiyayewa tare da yin biyayya ga matakan da masana kiwon lafiya suka sanya wajen dakile yaduwar cutar Corona.

A shekarun baya dai, kafin annobar Covid-19 ta bullo akan shafe kwanaki biyar ana gudanar da hidimomin al’ada na masarautar Kano a yayin bikin karamar sallah.

Hoton Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje da Sarkin Bichi Alhaji Aminu Ado Bayero.

Continue Reading

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 324,535 other subscribers.

Trending

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!