Connect with us

Labarai

Muna kashe sama da biliyan 50 na tallafin lantarki kowanne wata -Buhari

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ce a duk wata tana kashe sama da naira biliyan hamsin wajen bada tallafin samar da hasken wutar lantarki.

 

Ministan samar da hasken wutar lantarki Sale Mamman ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwar da mai bashi shawara kan harkokin yada labarai Mr. Aaron Artimas ya fitar a Abuja.

 

Aaron ya ce, Sale Mamman ya shaida hakan ne ga wata tawagar jagororin jaruman Hausa na Kannywood lokacin da suka kai masa ziyara a ofishinsa.

 

Minsitan ya ce, wadanann kudade da aka kashe wajen samar da wutar lantarki cikin wata guda, ya biyo bayan korafe-korafen da ake samu daga ‘yan Najeriya ga me da karin farashin wutar lantarki, wanda hakan ya sanya gwamnatin tarayya ta dauki nauyin kashe naira biliyan hamsin wajen samar da wadataccitar wutar ga ‘yan kasa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!