Addini
Hukumomi a kasar Saudia zasu dawowa da maniyyata kudaden su
Hukumomi a kasar Saudia Arabia, ta karkashin ma’aikatar aikin hajji, ta sanar da cewar zata biya al’umma kudin biza da takiti da ‘yan sauran kunji kunji na kudaden Umrah, sakamkon hana gudanar da aikin Umrah, da hukumomin kasar sukayi a yunkurin da suke na dakile yaduwar cutur Corona Virus, mai taken Covid 19.
Sanarwar takara da cewa, duk wanda ya biya kudin sa da niyyar yin umrah, hukumomin na Saudia, sun fara shiri na biyan kudin ta hanyar na’ura don haka a na kira ga al’umma da su tuntubi jami’an su da sukayi musu jagora wajen biyan kudaden wato Agents, don karbar hakkin su.
Sakamakon sanarwar, hukumar aikin Hajji ta kasa, NAHCON, tayi kira ga wanda suka biya kudaden su ta hannun jami’an da suke da halastaccen lasisi, dasu tuntubi jami’an don ganin sun samu kudaden su da zarar an fara biya.
Labarai masu alaka.
NAHCON: ta yi jigilar maniyatan aikin hajji dubu sittin da biyar a bana
An horar da daliban Aminu Kano yadda ake gudanar da aikin Hajji
Haka zalika hukumar tace duk wanda suke da matsala ko suke fuskantar ta wajen samun kudaden dasu kai korafin su wajen kwamishinan gudanarwar aikin Hajji, ta hanyar aiko sakon su ko kuma zuwa da kansu ofishin hukumar a Abuja, tare da cikakkun shaidun tabbatar da biya ta hannun jami’an da suke da Lasisi.
A wata sanarwa da jami’ar hulda da jama’a ta hukumar aikin Hajjin ta kasa, Fatima Sanda Usara, ta sakawa hannu tace hukumar a shirye take ta kare hakkin duk wani mai mu’amala da hukumar da kuma jami’an dake gudanar da aiki tare da ita.
Haka zalika hukumar, ta bada layin kira na wayar hannu da za’a kira don neman karin bayani.
Kamar haka …………. NAHCON: 08033826429
da kuma…………….. NAHCON: 07033701605
You must be logged in to post a comment Login