Connect with us

Addini

Matakai 4 don yaki da Coronavirus a musulunce – Sheikh Daurawa

Published

on

Fitaccen malamin addinin musulunci a Najeriya Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya bayyana wasu matakai hudu matsayin, hanyoyi kaifiyyan da za a bi kan annobar Coronavirus.

Malam Daurawa yayi wannan jawabi ne cikin hudubarsa ta yau jumu’a a masallacin sa dake unguwar Fagge Plaza.

Mataki na farko a cewar Malam Daurawa shi ne Imani da kaddara cewa abinda Allah kaddara shi ne zai faru, musulmi yayi Imani cewa mahalicci ne ke da ikon kaddara masa rayuwar sa.

Na biyu shi ne, mu yarda da hukuncin Allah na mutuwa ko rayuwa, don haka a duk sanda mutuwa ta zo sai mutum ya tafi ko da Coronavirus ko babu ita.

Mataki na uku, daukar matakan kariya, musamman abubuwan da jami’an lafiya suke ta fada, yakamata abi wadannan matakai sau da kafa.

Abu na hudu shi ne, jama’a ta kaucewa yada jita-jita, abubuwan da ake yadawa na karya game da Coronavirus sun yi yawa.

A lokacin annobar Ebola wani ya kirkiro cewa a yi wanka da gishiri, yanzu kuwa an yiwa Annabi (s.a.w) karya cewa wai wani mutum yayi mafarki ya ga manzon Allah (s.a.w) ya ce masa ya bude alkur’ani mai girma ya duba zai ga gashi, sai ya jika shi ne maganin Coronavirus.

Cikakken rahoton zai zo muku a shirin Inda Ranka na yau @9:30pm.

Karin labarai:

Covid-19: BUK ta umarci daliban dake zaune a makarantar su koma gidajen su

Ganduje : zan yi duk mai yuwa wajen hana COVID-19 shigowa Kano

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Addini

Za ayi zubeben kwarya tsakanin malaman Kano

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ce nan bada jimawa da zarar wucewar annobar Covid-19 za ta shirya wata gagarumar Mukabala a tsakanin bangarorin addini dake jihar, domin kawo karshen gutsiri-tsoma dake faruwa a tsakanin su.
Kwamishinan al’amuran addini na jihar Kano, Malam Muhammad Tahar Baba Impossible shi ne ya bayyana hakan yayin zantawarsa da wakilin mu Yusuf Ali Abdallah a yau Laraba.
Baba Impossible yace, biyo bayan takun saka da ake yawan samu kan batanci ga addini tare da wuce gona da iri daga wasu al’umma, ya sanya daukar wannan mataki domin rarrabewa da baccin makaho.
Har ila yau, Impossible ya ce, a kwanakin baya jami’an tsaron farin kaya DSS sun gayyaci dukkan bangarorin malaman addini dake jihar, inda ta gargadesu kan su ja kunnen mabiyansu wajen kaucewa daukar doka a hannu.

Karin labarai:

Baba Impossible ya musanta fatawar da Maigida Kacako ya bayar

Kowa yazo ya dauki dan sa daga makarantun Mari ko mu dauki mataki –Gwamnatin Kano

Continue Reading

Addini

Covid-19 Gwamnatin Saudia zata bude ofishin Fasfo

Published

on

Gwamnatin  kasar Saudia, ta  bude ofishin karbar fasfo a filin jirgin sama na Sarki Abdul Aziz, dake birnin Jeddah don shirin duba biza ta masu aikin Umarah.

Hakan ya biyo bayan tsare- tsaren da hukumomin a Saudia suke, na kammala aikin gyaran bizar wanda shaidar izinin zaman su a kasar  ya kare tare da kara wa’adin zaman su a kasar ta Saudia, da wanda suka nemi bizar ta kafar sadarwa ‘internet’ a ofishin ma’aikatar aikin Hajji da Umara.

Rahotanni sun tabbatar da cewar, a wani umarni da masarautar kasar ta bayar, an cire sunayen wanda suka je yin aikin Umara, da suka wuce wa’adin da aka dibar musu, da wanda suke da matsaloli na kudade, daga cikin wanda za’a tuhuma, ko cin tarar su , daga cikin hadakar wanda kasar ta Saudia zata tisa keyar su zuwa kasashen su na  Asali, sakamakon cewar sun samu tsaiko kasancewar bullar Cutar Corona Virus.

Labarai masu alaka.

Covid-19: Musulmai za su yi azumi kan Coronavirus

Covid-19: Al’ummar kasar nan su kwantar da hankalin su kan aikin Hajjin bana-Fakistan

Rahotannin sun kara da cewa ofishin fasfo din yace yin hakan na daga cikin umarni da kuma hadakar aiki tsakanin ma’aikatar aikin Hajjin kasar, da ma’aikatar Lafiya, da kuma ta harkokin jirgin sama, don dubawa da bibiyar hada- hadar shige da fice a cikin kasar , a gefe daya kuma tare da daukar matakan killace yaduwar cutar a fadin kasar.

 

Continue Reading

Addini

Musulmai sun yi taron addu’a kan Coronavirus a Kano

Published

on

Gidauniyar Sheikh Karibullah Nasiru Kabara, ta gudanar addu’a ta musamman dangane da cutar Corona Virus , da ta addabi al’ummar duniya baki daya.

Taron addu’ar ya samu halartar dumbin al’ummar Musulmi duk da kiraye -kirayen da masana harkokin kiwon lafiya ke yi , na rage mu’amala a cikin mutane don rage yaduwar cutar, an kuma gudanar da taron ne a rufafen dakin taro na filin wasa na Sani Abachi dake Kofar Mata.

Da yake jawabi a wajen taron addu’ar Shugaban Darikar Kadiriya na Africa, Sheikh Karibullah Nasiru Kabara, ya ce kaucewa tafarkin Ubangiji Allah (SAW) ya sanya yawaitar cututtuka masu addabar mutane ,kasancewar addinin Musulunci yazo da tsarin rayuwa mai inganci wacce da zarar an bi tafarkin ta zata datar da al’umma.

Karin labarai:

Kano : Ma’aikatu 2 za su hada kai don yaki da cutar Coronavirus

Kano: Babu rahoton bullar cutar COVID-19 -Dr, Aminu Tsanyawa

Sheikh Karibullah, ya yi kira ga al’umma da su ji tsoron Allah, tare da yawaita tuba da kula da tsaftar muhali domin kare kansu da kwayar cutar ta Corona.

A wajen taron Sarkin Kano Aminu Ado Bayero, wanda Dan Amar din Kano Alhaji Umar Shehu Harazimi, ya wakilce shi ya yi kira ga hakiman sa dasu yi duk mai yiwuwa wajen fadakarwa da gangamin wayar da kan jama’ar su don maganin cutar .

Shamsu Dau Abdullahi, wakilinmu da ya halarci taron addu’ar , ya rawaito cewa manyan malamai da sarakunan gargajiya da jami’an tsaro na daga cikin wanda suka hallarci taron addu’ar da ya gudana a yau Asabar .

Continue Reading

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 316,595 other subscribers.

Trending

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!