Ƙetare
Hukumomi Jamhuriyyar Benin sun daƙile yunƙurin juyin mulki

Ministan harkokin cikin gida na Jamhuriyar Benin ya bayyana a gidan talabijin ɗin ƙasar domin sanar da cewa yunƙurin juyin mulkin da wasu sojoji suka yi bai yi nasara ba.
Wani rukunin sojojin ƙasar ƙarƙashin Laftanar Kanar Pascal Tigri ya sanar da hamɓare Shugaba Patrice Talon tare da dakatar da tsarin mulki a kafar talabijin ɗin.
“Da safiyar Lahadi, 7 ga watan Disamban 2025, wasu tsurarin sojoji sun yi yunƙurin ƙwace mulki domin tayar da fitina a ƙasa da kuma ma’aikatu,” a cewar Minista Alassane Seidou.
“Ganin wannan lamari, sai rundunar sojan Benin, kamar yadda suka sha rantsuwa, suka ci gaba da mara wa ƙasarsu baya. Matakin da suka ɗauka ya ba su damar shawo kan lamarin kuma suka daƙile yunƙurin.”
You must be logged in to post a comment Login