Labarai
Hukumomi sun gaza samar da mafita kan noman rani -Garba Gidan Maza
Wani manomin rani daya shafe shekaru sama da arbain yana gudanarda Noma a Unguwar Gidan Maza a Kano Malam Garba Adali ya koka kan yadda har yanzu suka gaza samun cigaba a harkar noman rani musamman na rashin sabbin naurorin zamani sai dai suyi amfani da na gargajiya.
Garba Adall ya bayyana hakan ne a yayin zantawarsa da manema labarai yana mai cewa duk da irin yadda gwamnatin shugaba Buhari ke kokarin.
kamata ya yi a bunkasa harkar Noma amma ko kadan babu wani tallafi da suka taba samu daga gwamnatin tarayya a harkar noman su, a cewar Malam Garba Adali.
Gwamnatin tarayya ta yi yarjejeniya da shirin Sasakawa akan noma
Rikici ya barke tsakanin manoma da makiyaya a Kano
Gwamanti ta kebe fiye da bilyan goma don noman rani a Kano -Sani Bala
Malam Garba Adali ya kuma kara da cewa suna noma duk wasu nau’ikan kayan abinci, har ma da wanda turawa ke amfani da Su, amma matsalar rashin sabbin kayan zamani na noma nayi musu barazana sakamakon rashin karfin jarin da suke dashi.
Manomin ya kuma nanata cewa babbar matsalar da take ciwa manoman rani tuw0 a kwarya a yanzu bai wuce rashin takamaiman farashin kudin taki da suke fuskanta a wajen yan kasUwa ba. matukar ba kamfani aka je don siya ba, don haka akwai bukatar sanya hannun gwamnati.