Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Sarkin karaye ya rantsar da majalisar masarautar sa

Published

on

Sarkin Karaye Alhaji Ibrahim Abubakar na biyu ya rantsar da ‘yan majalisar masarautar tare da fara zaman majalisar na farko jiya a fadar sa dake Karaye.

Rantsarwar ta samu halartar shugabannin kananan Hukumomin yankunan dake karkashin masarautar da sauran manyan hakiman sa.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun masarautar Karaye Haruna Gunduwawa ya fitar aka rabawa manema labarai.

A Alhamis din makon da ya gabata ne dai Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya sanya hannu kan kudurin dokar kafa sabbin masarautun bayan sahalewa da majalisar jihar tayi a ranar.

Sarkin Karaye ya rushe majalisar masarautar sa

Gwamna Ganduje ya nada Sarkin Kano Muhammad Sunusi shugaban majalisar Sarakunan Jihar Kano

Sarkin Kano ya gana da masu zuba jari daga kasar Sin

Sanarwar ta kuma kara da cewa, Sarkin Karaye Alhaji Ibrahim Abubakar na biyu wanda kuma shine Shugaban majalisar ya godewa Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje bisa kokarin sa wajen bijiro da ci gaban masarautun da shakka babu zai kawo bunkasar yankunan su.

Mambobin majalisar masarautar ta Karaye sun hadar da Alhaji Isma’ila Gwarzo da Alhaji Jibrin Ibrahim Zarewa da Alhaji Lawan Sule Garo da Barista Balarabe Bello Rogo da Alhaji Sidi Mustapha Karaye da kuma Alhaji Wada Na Kofar Yamma.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!