Labarai
Hukumomin Habasha sun sanya dokar takaita zirga-zirga a yankin Amhara
Hukumomi a kasar Habasha, sun sanya dokar takaita zirga-zirga a yankin Amhara, biyo bayan zanga-zangar nuna adawa da yunkurin wargaza sojojin yankin, da gwamnatin kasar ke shirin yi.
Rahotonni sun bayyana cewa, An gudanar da zanga-zanga a garuruwa da dama na yankin Amhara tun bayan da gwamnatin kassar ta sanar da shirin shigar da rundunonin soji da wasu jihohi suka kafa, cikin rundunar soja ko ‘yan sanda ta tarayya.
Firaminista Abiy Ahmed ya ce, An dauki matakin ne saboda hadin kan kasar Habasha, inda ya yi gargadin cewa za a dauki matakan tabbatar da doka a kan duk wanda yake adawa da matakin gwamnati.
Wadannan dakarun yankin sun haifar da cece-kuce a baya, musamman a yankin Tigray da aka dauki tsawon shekaru ana gwabzawa da su, inda wadanda ke aiki a Amhara suka ba da taimako ga sojojin tarayya amma ana zarginsu da cin zarafin bil adama.
You must be logged in to post a comment Login