Labarai
Hukumomin tsaro sun ceto mutane 21 da aka yi garkuwa da su

Hukumomin tsaro sun ceto mutane 21 da aka yi garkuwa da su tare da cafke mutane hudu a Dutsen Dargaza da ke Karamar Hukumar Danmusa ta Jihar Katsina.
Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar Katsina, Dakta Nasir Mua’zu, ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar jiya Asabar.
Sanarwar ta bayyana cewa aikin ya gudana ne karkashin jagorancin Hukumar Tsaron Farin Kaya ta DSS tare da Sojoji, ’Yan Sanda da kuma jami’an sa kai, inda aka kama mutane hudu da ake zargi kuma ana ci gaba da binciken su.
Wadan da aka ceto sun hada da mata 16, maza biyu da jarirai uku da aka sace daga Gidan Sarkin Bayero da ke Karamar Hukumar Musawa da wasu wurare.
Sanarwar ta kara da cewa aikin ya mayar da hankali ne kan maboyar ɗan taʼadda Kamilu Chiroma wanda aka fi sani da Buzaru a Dutsen Dargaza.
Haka zalika sanarwar ta ce za a gurfanar da wadan da ake zargi a gaban kotu bayan kammala bincike.
You must be logged in to post a comment Login