Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Hukuncin da kotu ta yankewa Abdurrasheed Maina na kan tsarin doka – Barista Umar

Published

on

Wani lauya anan Kano ya bayyana hukuncin da aka zartarwa tsohon shugaban kwamitin gyaran Fansho na ƙasa Abdurrasheed Maina a matsayin abinda yake akan doka da tsari.

Barista Umar Isah Sulaiman ne ya bayyana hakan ta cikin wani shiri da ake gudanarwa a tashar Arewa FM da safiyar ranar Talata.

Barista Umar ya ce, laifukan da kotu ta samu Maina da shi sun saɓa da dokokin ƙasa musamman ma laifin halasta kuɗaɗen haram, da zamba cikin aminci.

“A Shari’a akwai abinda ake kira “Concorently” wato zaman shekaru ɗaya bayan ɗaya na adadin shekarun da kotu ta yankewa mai laifi”.

Lauyan ya ci gaba da cewa “Kotu ta yiwa Maina hukunci kamar haka: inda canjin farko zai shafe shekara 5 caji na biyu shekara 8 caji na uku shekara 3 sai na huɗu 8 na biyar 2 na shida 5 na bakwai 8 da sauran caje-caje”.

A cewar Barista Umar “Maina yana da damar ɗaukaka ƙara a cikin kwanakin da basu gaza 90 kafin hukuncin da aka yanke masa ya fara aiki”.

Sai dai ya ce, abin jira a gani bai wuce wanne hukunci kotun ɗaukaka ƙarar za ta yi ba, a kan hukuncin babbar kotun tarayyar duk da cewa an kama shi da laifukan kuma ya gaza kare kan sa.

“Gwamnati ta ƙiri-ƙiri kwamitin gyaran fansho ne domin duba yadda za a inganta rayuwar ƴan Fansho a ƙasar nan wanda ta ɗora alhakin ga shi Maina” a cewar Barista Umar.

A ranar Litinin 8 ga watan Nuwamba ne babbar kotun tarayya ƙarƙashin mai Shari’a Okong abang ta yankewa Abdurrasheed Maina hukuncin ɗaurin shekaru 61 a gidan gyaran hali bisa aikata laifukan almundahanar kuɗaɗe.

Sannan Kotun ta same shi da laifin ɓoye sunansa wajen buɗe asusu a bankin UBA da kuma Fidelity, inda ya ɓoye naira miliyan 300 sannan ya sake sanya naira miliyan 500, ya kuma ƙara sanya naira biliyan ɗaya da rabi.

Kotun ta ce waɗannan kuɗaɗe da ya ɓoye a bakunan ya kwashe su ne daga asusun kwamitin gyaran fansho da shugaban ƙasa ya kafa.

Haka zalika Kotun ta ce hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasa EFCC ta gabatar da gamsassun shaidun da suka tabbatar da cewa Abdulrashid Maina ya aikata laifin halasta kuɗaɗen haram da suka haura naira miliyan 171.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!