Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kotu ta yankewa ɗan Abdurrashed Maina hukuncin ɗaurin shekara 24

Published

on

Babbar kotun tarayya a birnin tarayy Abuja ta yanke wa Faisal ɗan tsohon shugaban kwamitin gyaran Fansho Abdulrasheed Maina hukuncin ɗaurin shekara 24 a gidan yari.

A zaman kotun na ranar Alhamis mai shari’a Okon Abang ya samu Faisal da Laifuka 3 da suka haɗar da halatta kuɗin haram, wanda hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa ta’annati EFCC ra tuhume shi da su.

Mai Shari’a Abang ya ce, EFCC ta gabatar da hujjojin da ke tabbatar da cewa Faisal ya yi amfani da wani asusun ajiya na banki na jabu a bankin UBA, inda ta nan ne mahaifinsa Maina ya yi almundanar kuɗi har naira miliyan 58 da dubu ɗari 1.

Kotun ta tabbatar da cewa an tura kuɗin ne ta wani asusu mai ɗauke da sunan Alhaji Faisal Farm 2, kuma Faisal da mahifinsa sun cire kuɗaɗen daga tsakanin Oktoban 2013 zuwa Yunin 2019.

Mai shari’ar ya yankewa Faisal hukuncin ɗaurin shekara 14 ne kan laifuka biyu, sai kuma shekara goma kan wasu laifuka biyu, duk da cewa bai halarci zaman kotun ba, har ma ake zargin cewa ya tsere zuwa wata ƙasar.

Sai dai hukuncin nasa na shekara 24  zai yi zaman gidan kaso na shekara 14 ne, dalilin yadda hukuncin za su tafi a tare.

Idan za a iya tunawa a watan Fabrairun 2021 ne Faisal ya tsere zuwa Amurka, inda a zaman kotun da aka yi na lokacin lauyan EFCC, Mohammed Abubakar, ya bayyana wa mai shari’a Okon Abang hakan.

Har ma kotun ta bayar da belin Faisal a kan kuɗi naira miliyan 60 da mai tsaya masa wanda zai kasance ɗan majalisar wakilai ne.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!