Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kotu ta yankewa matasa hukuncin shekara 16 bisa laifin damfara

Published

on

Babbar Kotun Jihar Kano mai lamba 4 da ke zamanta a Sakatariyar Audu Bako karkashin jagorancin mai shari’a Yusuf Muhammad Ubale, ta zartar da hukuncin dauri ga wasu mutane biyu da ta kama da laifin fashi da makami.

Mutanen da suka hada da Lawrence Nwora  da kuma Sunday David, an kama su da bindiga a hannunsu kirar Pistol, inda suka yi wa wani mai suna Alhaji Tukur Umar fashin kudi naira miliyan 2 da dubu 39, bayan ya fito daga wani Banki a unguwar Bompai a nan Kano.

Mutanen sun aikata laifin ne a ranar 28 ga watan Janairun shekarar 2011, laifin da ya saba da sashe na 97 da na 298 na kundin hukunta laifuka na Penal Code.

Mai gabatar da kara Barista Dalhatu Dada ya gabatar da shaidu guda biyar, yayin da wadanda ake karar suka kare kansu da kansu.

Mai shari’a Yusuf Muhammad ubale ya yankewa mutanen biyu hukuncin daurin shekaru goma sha biyar-biyar tare da tarar naira dubu 130 kan laifin fashi da makami.

Sai kuma hukuncin daurin watanni shida-shida ko kuma biyan tarar naira dubu 20 kan laifin hadin baki domin aikata laifi.

 

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!