Connect with us

Labaran Kano

Iftila’i: Dan KAROTA ya rasa ran sa

Published

on

Wani Jami’in hukumar karota ya gamu da ajalinsa lokacin da yake kokarin  kama wani mai karamar mota da ake zargin ya saba dokar titi a yankin Yan Dusa, dake dakata a nan Birnin Kano.

Ana dai zargin mai karamar motar ya bi ta kan ruwan cikin jami’in hukumar KAROTA ya kuma tsere.

Marigayin wanda ake kira da Tijjani Adamu na aiki ne a sashin ayyukan yau da kulluma na hukumar KAROTA yayin da ya gamu da iftala’in rasa ran sa.

Daga nan Freedom Radio mun tuntubi kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar DSP Abdullahi Haruna Kiyawa kan ko son sami wannan labarin.

Haruna Kiyawa ya ce tabbas sun sami labarin yayin da tuni suka fara tattara bayanai kan wannan batun.

Haka zalika kakakin hukumar KAROTA ta jihar Kano Nabulusi Abubakar Kofar Na’isa yace tuni hukumar ta dauki gawar ta mika ga jami’an ‘yan sanda kuma tuni aka mikata dakin ajiye gawarwaki na Asibitin Kwararru na Murtala.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 338,464 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!