Labarai
Iftila’i: Gobara ta tashi a kasuwar ƴan katako da ke Na’ibawa
Wata gobara ta tashi cikin dare a kasuwar ƴan katako da ke Na’ibawa Ƴan Lemo da tsakar daren jiya Asabar.
Wasu shaidun gani da ido sun shaida wa Freedom Radio cewa, wutar ta kama tun misalin ƙarfe 1 na dare kuma har kawo lokacin da muke haɗa wannan rahoto 5:30am ba a kai ga kashe wutar ba.
Jami’in yaɗa labarai na hukumar kashe gobara ta Kano Sa’idu Muhammad Ibrahim ya tabbatar wa da Freedom Radio faruwar lamarin.
Ya ce, “Mun samu kira daga wannan kasuwa ta ƴan katako da misalin ƙarfe 3:20 na dare, daga wani bawan Allah mai suna Hafizu Abdulƙadir”
Ya ci gaba da cewa, “Har kawo wannan lokaci 5:28am na asuba jami’an mu na tsaka da ƙoƙari domin kashe wannan gobara”.
Muhammad Ibrahim ya ce, kawo yanzu ba su kai ga gano musabbabin wannan gobara ba.
Ƙarin bayani zai zo nan gaba.
Cikin hotuna:
You must be logged in to post a comment Login