Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Gobara ta tashi a wani gidan mai dake Kano

Published

on

Gobarar dai ta tashi ne da misalin karfe 10 na dare, wadda ta shafe kusan sa’o’i biyu tana ci, duk da daukin da jami’an hukumar kashe gobara ta Jihar Kano da jami’an tsaro da kuma al’ummar gari su kai wurin.
A lokacin Freedom Radio ta ziyarci wurin, ta iske jama’a cikin dimuwa da kuma jami’an tsaro daban-daban a wurin ta ko ina, kasancewar wurin na da alaka da babbar tashar mota da aka fi sani da tashar Kuka, wadda ake jigilar fasinjoji daga nan Kano zuwa sauran jihohi da ma kasashen masu makwabtaka da kasar nan.
Baya ga kasuwar Kofar Ruwa wadda ta yi fice a Arewacin Najeriya.
Freedom Radio ta zanta da wasu da wasu shaidun gani da ido, wadanda su ka ce tashin gobarar ya haifar da gudun tsira da rai a tsakanin jama’a.

Wani kwandastan mota a tashar ta Kofar Ruwa ya ce, sun yi hadin gwiwa da jami’an sintiri wajen tseratar da fasinjojin da suka shiga firgici sanadiyyar gobarar.

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce ya zuwa lokacin da muke hada wannan rahoto tana ci gaba da tattara bayanai domin gano musabbabi da kuma asarar da gobarar ta haifar, kamar yadda kakakin hukumar Sa’idu Muhammad Ibrahim ya bayyana.

A wani bangaren kuma rahotonni na cewa an samu wasu bata-gari da suka yi kokarin kutsawa cikin kasuwar ta Kofar Ruwa domin yin sata, sai dai jami’an ‘yan sanda da jami’an sinturi sun yi kokarin korarsu tare da tsare dukiyoyin al’umma.
A kan hakan ne muka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano DSP. Abdullahi Haruna Kiyawa, wanda ya tabbatar da faruwar al’amarin.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!