Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Iftila’I: Mutane biyar sun mutu a Kano yayin hakar kasa

Published

on

Hukumar kashe gobara ta jihar kano, ta tabbatar da mutuwar wasu Matasa biyar da suke tsaka da diban kasa domin bayar da gudunmawa ga abokinsu da ke shirin yin aure a wani rami dake Kauyen ‘yan Lami a karamar Hukumar Bichi.

Sanarwar hakan ta biyo ne ta bakin Jami’in hulda da jama’a na hukumar da ke nan kano SFS Saminu Yusuf Abdullahi.

Ya ce lamarin ya farune a ranar Asabar 3 ga Maris da muke ciki , yana mai cewa lokacin da jami’an su suka isa wurin sun iske gawar matasa biyar a ramin da iftila’in ya rutsa da su.

Cikin wadanda lamarin ya shafa sun hada da Alasan Abdulhamid mai shekaru 22 da Muhammad Sulaiman mai shekaru 35 da Dauda Nasir dan shekara 25

Sauran sune Jibrin Musa mai shekaru 30 da kuma Jafaru Abdulwahabu mai shekaru 30.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar SFS Saminu Yusuf Abdullahi ya kuma ce tuni hukumar ta mika Mamata ga dagacin garin na ‘yan Lami domin yi musu jana’iza kamar yadda addinin musulnci ya ta nada.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!