Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Ighalo, Chukwueze da Oshola za su gudanar da tattaki na gidauniyar Kanu

Published

on

Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta kasa Super Eagles, Samuel Chukwueze ya ce zaiyi tattaki da tsohon Dan wasan Najeriya Nwankwo Kanu a wani bangare na bikin ranar tunawa da masu ciwon Zuciya.

Chukwueze mai shekaru 22 dake wasa a kungiyar kwallon kafa ta Villarreal dake kasar Spain ya fitar da wani gajeran Bidiyo a shafukansa na sada zuminchi dake kiran al’ummar kasar nan kan su fito ayi tattakin da su domin nuna damu ga wadan da ke dauke da cutar.

Silas Nwanko ya zama gwarzon dan wasan NPFL na 2021

Ya ce tattakin da za’ai mai tsawon kilo mita 10 za’a gudanar da shi a ranar 29 ga watan da muke ciki na Satumba a birnin tarayya Abuja.

Haka zalika shima tsohon dan wasan kasar nan, da Manchester United, Odion Ighalo yabi sahun mutanan da za su yi tattakin inda yake kiran ‘yan wasan kungiyar kwallon kafar ta Najeriya Super Eagles da su shigo tattakin da Nwankwo Kanu zai Jagoranta.

Kazalika itama ‘yar wasan kungiyar kwallon kafar mata ta kasa Super Falcons, Azizat Oshoala ta ce za ta kasance cikin al’ummar da za su yi tattakin a ranar ta 29 ga watan na Satumba, domin nuna goyan baya da tunawa da masu dauke da ciwon na zuciya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!