Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Ighalo ya zura kwallo a wasan da AL Hilal ta doke AL Jazira da ci 6-1

Published

on

Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta AL Hilal Odian Ighalo ya yi nasarar zura kwallo a wasan da sukai nasara da ci 6-1 a kan Abu Dhabi a wasan gasar kasashen kungiyoyin duniya na FIFA Club World Cup.

Wasan dai ya gudana a ranar Lahadi 06 ga Fabrairun 2022 da muke ciki, wanda hakan ya baiwa kungiyar damar buga wasan kusa da karshe da Chelsea.

Odian Ighalo dai shi ne ya fara zura kwallon farko a minti na 14 bayan samun taimakon Abdoulay Diaby.

Tawagar Al Jazira dai itace ta lashe gasar kwararru ta UAE ta hadaddiyar daular larabawa ta kakar wasannin shekarar 2020/2021.

Zuwa yanzu dai kungiyar kwallon kafa ta Al Hilal zata kece raini da zakarun gasar kofin nahiyar turai Chelsea a zagaye na hudu a ranar Laraba mai zuwa.

Yayinda AL Jazira zata fafata da Monterrey a neman gurbin mataki na biyar a gasar da ake gudanarwa a kasar Dubai.

Gasar dai ta shekarar 2021 itace karo na 18 wadda ta kunshi kungiyoyin kasashen nahiyoyin duniya shida da suke fafatawa a wasanni daban-daban.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!