Addini
Ilimantar da mata kamar ilimantar da al’umma ne- wani malamin addini
An bayyana hakkin malami a kan dalibi da kuma hakkin dalibi a kan malami a matsayin wani babban abinda ya kamata kowace makaranta ta baiwa fifiko musamman ma makarantun Islamiyya.
Wannnan ya fito ne daga bakin wani malamin addinin musulunci da ke Hotoron Arewa, Malam Abdussalam Aliyu a jawabin da ya gabatar a wajen bikin saukar Al’Qurani da makarantar Dau’ul Huda, Islamiyya ta gudanar a unguwar Hotoron Arewa.
Malamin ya ce dole ne mazaje, musamman ma gidanta su jajirce wajen ganin mata sun samu ilimi, ta yadda zasu baiwa ‘ya’yansu tarbiyya mai kyau.
Da take jawabi, shugabar makarantar, Malama Aisha Sulaiman ta ce suna kokari sosai wajen ganin mata sun samu ilimin addinin musulunci musamman ma ilimin zamantakewar aure.
Wakilinmu Muhammad Lawan Rano ya ruwaito cewa, a yayin taron an baiwa dalibai maza da mata da suka hada matan aure 37 shaidar saukar karatun Al’qur’ani mai girma.