Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Addini

Yau Sheikh Jafar ke cika shekaru 14 da rasuwa

Published

on

A ranar 13 ga watan Afrilun 2007 Allah ya yiwa fitaccen malamin addinin musuluncin nan da ke Kano, Sheikh Jafar Mahmud Adam rasuwa.

 

Shehin malamin ya rasa ransa ne lokacin da ya ke jagorantar sallar asubahi a masallacin Almuntada da ke Dorayi a Kano, bayan da ‘yan bindiga suka bindige-shi.

 

An-haifi marigayi Sheikh Jafar Mahmud Adam a garin Daura da ke jihar Katsina a cikin shekarun 1960. Marigayi Jafar ya fara karatun allo a gidansu da ke Daura a wurin mijin yayar sa mai suna Malam Haruna, wanda kuma dan uwa ne na jini gare shi.

 

Daga nan kuma sai aka mayar da shi wajen wani malami mai suna Malam Umaru a wani gari wai shi “Koza” da ke arewa da Daura.

 

Daga bisani sun dawo Kano tare da malamin nasa a 1971, inda ya zauna a makarantar Malam Abdullahi a unguwar Fagge.

 

 

Rahotanni sun ce dama can Sheikh Jafar ya fara haddar alkur’ani mai girma, wanda ya kammala a shekara ta 1978.

 

Bayan ya yi haddar Alkur’ani sai kuma ya shiga makarantar boko a 1980.

 

Sheikh Jafar ya shiga makarantar koyon harshen Larabci ta mutanen kasar Misra a cibiyar yada al’adun kasar Masar da ke Kano (Egyptian Cultural Centre), sannan kuma ya shiga makarantar boko ta manya watau “Adult Evening Classes.”

 

A 1983 ne malamin ya kammala wadannan makarantu 2 na boko dana arabiya, wanda daga nan ya samu shiga makarantar GATC Gwale a 1984, inda ya kammala a1988.

 

Bayan shekara guda ne a 1989 ya wuce Jami’ar musulunci ta Madina.

 

A wannan babbar jami’ar musulunci ta Madinah ne malamin ya karanci ilimin tafsiri da Ulumul Kur’an, wanda kuma ya kammala a shekara ta 1993.

 

Tun a waccan lokacin ne kuma aka fara jin tafsirin sa na Al-Qur’ani a cikin garin Maiduguri da ke jihar Borno.

 

Haka zalika daga bisani Sheikh Jafar Mahmud Adam ya samu damar kammala karatunsa na digiri na biyu (Masters) a Jami’ar Musulunci ta Oundurman a kasar Sudan.

 

Haka kuma kafin rasuwar sa, ya yi nisa wajen karatunsa na digiri na uku (Phd) a Jami’ar Usman Danfodio da ke Sokoto.

 

 

Daga cikin karatun da malam ya karantar da su, sun hada da: tafsirin Alkur’ani mai girma.

 

Sheikh Jafar Mahmud Adam ya sauke Al-qur’ani mai girma kusan sau 2 a masallacin Muhammadu Indimi da ke cikin garin Maiduguri a jihar Borno.

 

Bugu da kari, ya kuma karantar da Kitabut-tauhid na Sheikh Muhammad Ibn Abdulwahab, da kuma litattafan hadisai na Umdatul Ahkaam, Arba’una Hadiith. Sauran darussan sun hada da wani litafin tauhidi da ya yi fice mai suna Kashfush-shubuhat.

 

Haka kuma Malam Jafar Mahmud Adam ya karantar da litattafan Bulugul Maram, Riyadussalihin, Siratun Nabawiy, da kuma Ahkamul Jana’iz, Sifatus Salatun Nabiy na Muhammad NasirudDeen Albany.

 

Tarihi dai ba zai taba mantawa da irin gudunmawa da Sheikh Jafar Mahmud Adam ya bai wa addinin musulunci ba, a Nigeria, Nahiyyar Afrika dama duniya baki daya.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!