Labaran Kano
Ilimin sana’o’i shi ne mafita ga al’umma
Shugaban sashen kula da al’amuran dalibai na jami’ar Yusuf Maitama Sule ta Kano Dr Yusuf Musa Kibiya, ya bayyana cewa fito da tsarin koyar da dalibai sana’o’in dogaro da kai da gwamnatin tarayya ta yi abu ne mai matukar alfanu la’akari da irin yadda dalibai da dama suka rungumi sana’o’in dogaro da kai sabanin a baya da suke jiran sai sun samu aikin gwamnati ko kuma wani aiki mai gwabi.
Dr Yusuf Musa Kibiya, ya bayyana hakan ne ta cikin shirin’’Duniyar mu a Yau’’ na nan Freedom Radio, da ya mayar da hankali kan yadda ake koyar da daliban jami’oi da kwalejoji sana’o’i.
Ya ce a baya daliban da suka kammala karatun Digiri da sauran fannoni na jira har sai gwamnati ta basu aikin yi, wanda dalilin samun yawan masu neman aikin ya sa gwamnati ta fito da tsarin domin rage zaman kashe wando.
Da yake tsokaci ta cikin shirin, Daraktan koyar da sana’o’i a makarantar kimiyya da fasaha ta jihar Kano Dr, Umar Muhammad Garzali da ya kasance a cikin shirin cewa ya yi, gwamnatin tarayya ta samar da manhajar koyar da sana’o’in ne tare da rarraba ta kashi-kashi ta yadda daliban za su amfana matuka da shirin.
Shi kuwa wani matashi mai gudanar da sana’ar dinki Muhammad Musa Abdullahi, ya ce ya kware a sana’ar ta Dinki ne sakamakon horon da ya samu a makaranta karkashin tsarin koyar da matasan sana’o’i a makaranta.
Ita ma wata mai gudanar da sana’ar Girke-girke da aikin kawata wuraren biki Sadiya Hashim Sabo, ta bayyana cewa, ta koyi sana’ar ne a kwalejin fasaha inda a yanzu haka ma take koyar da sana’ar yayin da kuma take yaye dalibai a halin yanzu.
Haka kuma ta kara da cewa malama nasu sun koya musu dabarun gudanar da kasuwanci baya ga sana’o’in inda hakan ya zamo mata jagora wajen cigaban kasuwancin na ta.