Connect with us

Labarai

Immigration : Ta kafa kwamitin kwararru na yaki da masu fasa kwauri

Published

on

Shugaban hukumar yaki da fasa kauri ta kasa, Muhammad Babandede ya kafa wani kwamitin kwararru da zai yi yaki da masu fasakwauri a kasar nan.

Hakan na cikin sanarwar da mai magana da yawun hukumar Mr Sunday James ya fitar a yau.

Sanarwar ta bayyana cewa an bai wa kwamitin damar ziyartar jihohin kasar nan don tabbatar da sun dakile laifukan masu fasakwauri.

Sanarwar ta kara da cewa, hukumar ta bunkasa ayyukanta ta hanyar ci gaba da yiwa masu tafiye-tafiye fasfo na E-migrant don tattara bayanan wadanda ke shige da fice a kasar nan.

Muhammad Babandede, ta cikin sanarwar, ya kuma ce, hakan zai taimakawa jami’an tsaro wajen kare rayuka da dukiyoyin al’ummar kasar nan.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!