Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Shugaba Buhari ya jagoranci zaman majalisar zartaswa a yau

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagorantci taron majalisar zartaswa ta kasa a yau Laraba, wanda aka gabatar ta kafar Internet.

Kafin fara taron sai da mahalratrsa suka don gudanar da adduo’i na musamman   don karrama wasu tsofaffin ministoci biyu da suka rasu a baya-bayan nan.

Tsofaffin ministocin sun hada da: Rear Admiral Olufemi Olumide da kuma Manjo janar Sam Momah.

Marigayi Olumide dai ya taba ya rike mukamin kwamishinan sufuri da ayyuka na tarayya a zamanin mulkin Yakubu Gawon da kuma Murtala Muhammad, yayin da Marigayi Sam Momah ya taba rike mukamin ministan ilimin kimiyya da fasaha a lokacin shugabancin marigayi janar Sani Abacha.

Cikin ministocin da suka hallara a zauren majalisar sun hada da, Ministan kudi kasafi da tsare tsare Hajiya Zainab Ahmad da ministan tama da karafa Sanata  Olamilekan Adegbite da kuma Attoni Janar kuma ministan shari’a  Abubakar Malami.

Sauran sun hada da Ministan yada labarai da raya al’adu Alhaji Lai Muhammad da ministan lafiya Dr Osagie Ehanire da Adeleke Mamora da kuma ministan Muhalli, Alhaji Muhammad Mahmud.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!