Ƙetare
Ina da yaƙinin samar da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza- Trump

Shugaban Amurka Donald Trump, ya ce, ya na da yaƙinin samar da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza.
Shugaba Donald Trump, ya bayyana hakan ne a ganawarsa da Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu a Litinin din makon nan.
Masu shiga tsakani sun ce, a lokacin ganawar ne Netanyahu ya kira Firaministan Qatar Mohammed bin Abdulrahman bin Jassim Al Thani daga fadar White House na gwamnatin Amurka, inda ya nemi afuwa kan hare-haren da ya ƙaddamar a ƙasar kan masu shiga tsakani na Hamas.
Ana ganin dai wannan na cikin tsare-tsare guda 21 da Amurka ta tsara, waɗanda Netanyahu ya ce, suna yin nazari a kansu.
Ana tunanin daga ciki akwai janye sojojin Isra’ila daga yankunan da ta mamaye, sannan Isra’ila ta amince da ƙasar Falasɗinu, ita kuma Hamas ta sako waɗanda ta yi garukuwa da su a cikin kwana biyu ba tare da illa ba.
You must be logged in to post a comment Login