Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ina kan kudiri-na, na fitar da ‘yan Najeriya miliyan 100 daga kangin talauci – Buhari

Published

on

Gwamnatin tarayya ta kara jaddada matsayinta na fitar da ‘yan Najeriya akalla miliyan 100 daga kangin talauci nan da ‘yan shekaru masu zuwa.

 

A cewar gwamnatin, daya daga cikin manufofin da ta bullo da su don cimma kudirinta shine, kaddamar da shirin bunkasa makamashin gas (National Gas Expansion Program).

 

Karamin ministan man fetur Chief Timipre Sylva ne ya bayyana haka lokacin da ya ke jagorantar bikin bude taron tuntuba kan shirin bunkasa makamashin Gas a jihar Imo.

 

Ya ce shiriin zai samarwa miliyoyin ‘yan Najeriya aikin yi musamman matasa, wadadan za a basu horo na musamman yadda za su dogara da kansu.

 

A cewar ministan tun farko shugaba Buhari ya sanya shirin cikin tsarinsa na kakkabe talauci tsakanin al’ummar kasar nan kafin nan zuwa shekarun 2030.

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!