Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kaduna

PDP: Za mu sasanta Tambuwal, Kwankwaso, Aminu Wali

Published

on

Jam’iyyar PDP ta kasa ta kammala shirye-shirye don sasanta gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal da tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da kuma tsohon ministan harkokin kasashen wajen kasar nan Ambasada Aminu Wali.

 

An dai samu sabani tsakanin manyan masu fada aji a jam’iyyar ta PDP a yankin arewa maso yamma ne yayin zaben shugabannin shiyyar da aka gudanar a makon jiya.

 

Rahotanni sun ce, an yi taho mu gama tsakanin magoya bayan tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da magoya bayan gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal a yayin zaben shugabannin yankin arewa maso yamma na jam’iyyar ta PDP a garin Kaduna, wanda sanadiyar haka aka dakatar da zaben.

 

Wata majiya ta shaidawa jaridar Daily Trust cewa, tuni wasu magabatan jam’iyyar suka fara tattauna hanyoyin da za abi don magance rikicin da ke tsakanin ‘yan siyasar uku.

 

Majiyar ta kuma ce rikicin ya barke ne sakamakon mukamin mataimakin shugaban jam’iyyar shiyyar arewa maso yamma wanda aka warewa jihar Kano.

 

Mai magana da yawun jam’iyyar PDP Kola Ologbondiyan ya tabbatar da cewa tuni jam’iyyar ta fara shirye-shiryen sasanta manyan ‘yan siyasar yankin na arewa maso yamma.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!