Connect with us

Kowane Gauta

Muna neman afuwar ‘yan Najeriyar da suka tallata APC – Magaji Yalawa

Published

on

Dattijo Magaji Yalawa ya nemi afuwar wadanda suka yi tallan jam’iyyar APC suka kuma zaba, saboda gwamnatin shugaba Buhari ta gaza karara.

Magaji Yalawa ya bayyana hakan ne ta cikin shirin Kowane Gauta na gidan Radio Freedom, yana mai cewa a cikin kaso dari na masoyan Buhari a yanzu bai fi kaso biyar ya rage ba domin duk sun dawo daga rakiyar gwamnatin sa.

Dattijo Magaji ya kara da cewa ‘yan Najeriya sun yi imanin idan gwamnatin Shugaba Buhari ta hau zata kawo sauyi mai kyau ga ‘yan kasa, amma sai suka fuskanci babu wani sauki da za su iya samu a gwamnatin Buhari.

Yace duk irin alkawuran da suka yiwa mutane musamman na yaki da ‘yan ta’adda da fashi da makami musamman a lokacin yakin neman zabe, gwamnatin Buhari ta gaza cimma wannan nasarorin.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 335,289 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!