Labarai
INEC ta cire sunan Sanata David Mark a matsayin shugaban jam’iyyar ADC

Hukumar zaɓen Najeriya, INEC ta cire sunan Sanata David Mark a matsayin shugaban jam’iyyar ADC tare da Abdulra’uf Aregbesola a matsayin sakatare janar na jam’iyyar daga na’urarta.
A wata sanarwa da ta fitar ranar Laraba, Inec ta ce ta ɗauki matakin hakan ne sakamakon hukuncin kotun ƙoli da kuma shari’ar da ke gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja dangane da rikicin da ake yi tsakanin ɓangarori biyu wato David Mark da na Nafi’u Gombe.
A wani hukunci da kotun ɗaukaka ƙara ta yanke ranar 12 ga watan Maris ɗin 2026, kotun ta nemi dukkannin ɓangarorin da su jira hukuncin babbar kotun tarayya.
Hukumar ta zaɓe ta ce sakamakon hukuncin na kotun ɗaukaka ƙarar ne ta karɓi ƙorafe-ƙorafe daga lauyoyin ɓangarorin biyu masu taƙaddama da juna a kotu, inda ɓangaren David Mark ya nemi ka da ta amince da ɓangaren Nafi’u Gombe sannan shi ma lauyoyin Gombe suka nemi a cire sunan David Mark daga na’urarta ta jerin shugabannin jam’iyyun da Inec ta amince da su.
Rikicin dai ya samo asali ne a watan Yulin 2025 lokacin da shugabancin jam’iyyar ta ADC ya yi murabus inda kuma David Mark ya zamo shugaba.
Sai dai kuma tsohon mataimakin jam’iyyar, Nafi’u Gombe ya ƙalubalanci zaɓen inda ya dage cewa dole ne a samar da shugabanci ta hanyar da kundin tsarin mulkin jam’iyyar ya tsara.
You must be logged in to post a comment Login