Labarai
INEC ta dakatar da shirin sabunta rijistar masu zaɓe

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa INEC ta umarci duka kwamishinoninta da su dakatar da shirin sabunta rijistar zaɓe.
A makon jiya ne hukumat INEC ta fitar da sanarwar cewa, za a sabuntawa masu zaɓe rijista cikin kwanaki 45, a wani mataki na shirye-shiryen tun karar zaɓen 2027.
Sabunta katin zai shafi mutanen da suka yi rijinsta ne tsakanin 2011 zuwa 2024.
Wata sanarwa da Sakatariyar hukumar ta INEC Rose Oriaran-Anthony ta fitar ta ce, an dakatar da shirin tare da umartar duka kwamishinoninta da su dakata har sai zuwa ranar Alhamis 9 ga watan Afrilun da muke ciki inda za su gudanar da taronsu ta intanet domin sanin mataki na gaba.
You must be logged in to post a comment Login