Labarai
INEC ta gargadi masu yunkurin kawo mata cikas a zaben gwamnan Anmabra

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta gargadi mutanen dake yunkurin gurgunta shirin ta na gudanar da sahihin zaben gwamnan jihar Anmabra da za’a gudanar ranar Asabar mai zuwa 8 ga wannan watan Nuwamba.
A cewar shugaban hukumar Farfesa Joash Amupitan sun shirya tsaf don tabbatar da zaben kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar nan ya sahale.
A wata sanarwa da sakataran yada labaran shugaban hukumar Dayo Oketola ya fitar ya ce shugaban hukumar ya bayyana dukkan masu ruwa da tsaki tabbacin yin zabe mai cike da tsafta cikin tsarin gudanarwa.
Haka kuma ya bukaci masu ruwa da tsakin jihar dasu kasance masu aiki tare, kamar yadda aka samar da cikakken tsarin tsaro kafin da ya yin da kuma bayan kammala zaben.
You must be logged in to post a comment Login