Labarai
INEC zata daukaka kara kan hukuncin kotu
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta ce zata daukaka kara zuwa kotun koli kan hukunci masu cin karo da juna da kotun dukaka kara ta yanke a kwanakin bayan kan soke wasu jam’iyyu da ta yi.
Shugaban hukumar ya bayyana hakan ta bakin mai magana da yawun hukumar Festus Okoye cewa tabbas hukumar ba zata yi kasa a gwiwa ba wajen dauka kara kan wannan hukuncin.
Kazalika Festus Okoye ya ce hakika INEC ta karbi hukuncin da kotun daukaka kara ta yi a jiya Litinin 10 ga wannan wata na Agusta, wacce jam’iyyar ACD da wasu jam’iyyu 22 suka shigar gaban ta.
A cikin hukuncin da kotun daukaka karar ta yanke ta bayyana cewar hukumar ta INEC bata da karfin soke rajistar jam’iyar ACD da sauran jam’iyyu 22, ya yin da bata umarnin da ta sake yi musu rijista.
You must be logged in to post a comment Login