Connect with us

Labarai

Hukumar EFCC zata daukaka kara kan batun rufe asusun gwamnatin jihar Benue

Published

on

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa EFCC zata dauka ka karar kan hukuncin da babbar kotun tarayya na rufe asusun gwamnatin jihar Benue.

Wannan na kunshe cikin sanarwar da mai Magana da yawon hukumar ta EFCC Tony Orilade ya fitar cewa hukuncin da mai shari’a Mobolaji Olajuwon ya yanke a babbanr kotun dake birnin Makurdi ta jihar Beneu wace gwamnatin jihar ta nemi hukumar EFCC ta biya ta kudin diyya na bata mata suna na Naira miliyan 50 da kuma wasu bankunan kasuwanci guda 2 suma su biya Naira miliyan 25.

A dai watan Agustan bara ne sashin bincike na hukumar EFCC  ya bada umarnin da a rufe asusun kudi na gwamnatin jihar na wucin gadi.

Sai dai mai Magana da yawon hukumar ta EFCC ya ce lauyoyin hukumar na yi duk mai yuwa wajen daukaka kara don kalubalantar hukuncin da kotun ta yanke.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 338,465 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!