Labarai
INEC:Shugaba Buhari ya lashe zaben jihar Kano
Hukumar zabe ta kasa INEC ta bayyana Shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin wanda ya samu nasara a jihar Kano a zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar Asabar ashirin da uku ga watan da muke ciki na Fabrairu.
Da ya ke sanar da sakamakon zaben, babban jami’in tattara sakamakon zaben shugaban kasa a jihar Kano, farfesa Magaji Garba, ya ce Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC ya samu kuri’u miliyan daya da dubu dari hudu da sittin da hudu da dari bakwai da sittin da takwas.
Yayin da dan takaran jam’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar, ya zo na biyu da kuri’u dubu dari uku da casa’in da daya da dari biyar da casa’in da uku.
A cewar sa, adadin mutane miliyan biyar da dubu dari uku da casa’in da daya da dari biyar da tamanin da daya ne su ke da rajistar zabe na dindindin, yayin da miliyan biyu da dubu shida da dari hudu da goma aka tantance su domin kada kuri’ar.
Farfesa Magaji Garba ya kara da cewa, mutane miliyan daya da dubu dari tara da sittin da hudu da dari bakwai da hamsin da daya ne suka samu nasarar kada kuri’ar.