Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Inganta harkokin ‘yan sanda zai kawo sauyi a yaƙi da matsalar tsaro

Published

on

Tsohon mataimakin sufeto janar na ƙasa Muhammad Hadi Zarewa mai ritaya ya ce a wannan lokacin aikin ƴan sada ya canja ba kamar yadda aka sanshi abaya ba.

AIG Hadi Zarewa ya ce a baya aikin ‘yan sanda anayin sa ne cikin kwanciyar hankali inda yasha bambam da yanzu.

Muhammad Hadi Zarewa ya bayyana hakanne a yayin zantawarsa da Freedom Radio.

Zarewa ya kara da cewa abinda ya sa ake samun matsala da ƴan sanda a yanzu shi ne rashin basu kulawa yadda ya dace, wanda ke sa su karɓar na goro.

Zarewa ya ce da kasar nan zata inganta harkar albashinsu tare da basu kayan aiki yadda ya dace, da sauran abubuwa da zasu sanya su karsashi a aikin na su,to da hakan zai samar da ingantaccen aiki kamar yadda yake a baya.

Ya ce “shekarun baya al umma tsoron masu ɗammara suke,sakamakon yadda suke rike da aikin su yadda ya kamata, tare da tabbatar da shi a duk inda suke”

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!