Connect with us

Labarai

Tsaftar muhalli: An rufe kamfanin ɗura iskar gas a Challawa

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta rufe wani kamfanin ɗura iskar gas a yankin Challawa tare da cin tarar su tarar Naira dubu ɗari 5.

An rufe kamfanin mai suna United Gas sakamakon karya dokar tsaftar muhalli.

Kwamishinan muhalli Dakta Kabiru Ibrahim Getso ne ya bada umarnin rufe shi tare da cin tarar Naira dubu ɗari biyar.

Kamfanin dai ya ɓude tare da ci gaba da ayyukan sa a safiyar Asabar ɗin nan, daidai lokacin da ake tsaka da gudanar da tsaftar muhalli.

Kamfanin zai ci gaba da zama a rufe har sai sun cika ƙa’idar da gwamnati za ta gindaya.

Kazalika tawagar zaftar muhallin ta ci tarar waɗanda suka karya doka nan take, da adadin tarar ya kai dubu ɗari shida da uku.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!