Connect with us

Labarai

Najeriya na buƙatar ƙwararrun injiniyoyi domin gogayya da duniya – NSE

Published

on

Ƙungiyar Injiniyoyi ta Najeriya, NSE, reshen Jami’ar Aliko Dangote da ke Wudil, ta yi kira ga gwamnatoci a matakai daban-daban da su ƙara zuba jari wajen bunƙasa fannin injiniya a ƙasar.

Ƙungiyar ta ce hakan zai taimaka wajen samar da ƙwararrun injiniyoyi da za su taimaka wa Najeriya wajen samun ci gaba da kuma yin gogayya da sauran ƙasashen duniya.

Kiran ya fito ne yayin babban taron shekara-shekara na ƙungiyar na shekarar 2026, inda aka zaɓi sabbin shugabannin reshen tare da cike dukkan muƙaman zartarwa.

Injiniya Mohammed Musbahu Abdulkadir ne aka zaɓa a matsayin shugaban reshen, yayin da Injiniya Kabiru Ahmad Kwalli ya zama mataimakinsa. Injiniya Farfesa Ado Ma’aruf kuma ya zama babban sakatare, yayin da Injiniya Naziru Ado Osi ya zama mataimakin sakatare. Sauran shugabannin sun haɗa da Injiniya Mustapha Khalil a matsayin ma’aji, da Injiniya Dakta Shamsu Tukur Auwal a matsayin sakataren kuɗi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!