Ƙetare
Iran ta ɗage taron jana’izar Ayatollah Ali Khamenei

Kafar yaɗa labaran Iran sun ce an ɗage taron jana’izar Jagoran addinin ƙasar, Ayatollah Ali Khamenei, wanda aka shirya gudanarwa a daren yau Laraba a Tehran a Masallacin Imam Khomeini.
Dalilin ɗage taron shi ne “fargabar miliyoyin mutanen da za su halarci taron da kuma buƙatar yin shiri na musamman domin wannan adadi na jama’a da kuma yadda za a tsara taron cikin tsari mai dacewa.
An kashe jagoran Iran ɗin ne a harin haɗin gwiwar da Amurka da Isra’ila suka kai a ranar Asabar, wanda ya janyo tashin hankali da rikici mai tsanani a yankin Gabas ta Tsakiya.
Ba a bayyana sabuwar ranar da za a gudanar da taron jana’izar ba.
You must be logged in to post a comment Login