Connect with us

Ƙetare

Iran ta kai hari kan sansanin sojin Amurkan a Bahrain

Published

on

Dakarun juyin juya halin Iran, IGRC sun ce sun kai harin ”manyan makamai” masu linzami kan sansanin sojin Amurka da ke Bahrain.

IRGC ta ce ta kai harin ne a matsayin martani ga wasu rahotanni da ba a tabbatar da su ba na cewa Amurka ta kai hari a wata cibiyar tace ruwa sha a wani tsibiri da ke mashigin Hormuz.

“A matsayin martani ga harin da Amurka ta kai daga sansanin Juffair a kan tashar Qeshm, wannan sansanin na Amurka ya fuskanci mummunan hari daga rundunar IGRC”, a cewar wata sanarwa da IGRC ta fitar ta hanyar kafar yaɗa labaran Fasrna mai alaƙa da IGRC.

A halin da ake ciki kuma, ana jin ƙarar sautin na’urorin ankararwa a Bahrain, inda ma’aikatar harkokin cikin gida ta ƙasar ta buƙaci ‘yan ƙasar da mazauna yankin su nufi wani wurin ɓuya mai aminci.

A cikin ‘yan mintoci da suka gabata ne ma’aikatar cikin gidan Bahrain ta wallafa a shafinta na X cewa an samu tashin gobara da ƙonewar wasu gine-gine a Manama, babban birnin Bahrain, inda ta ce jami’an kashe gobara na ƙoƙarin kashe wutar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!