Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Mutane 24 sun rasa rayukan su sakamakon cin guba a abinci a Sokoto

Published

on

Gwamnatin jihar Sokoto ta tabbatar da mutuwar wasu iyalai 24 sakamakon cin abinci mai guba.

Kwamishinan lafiya Dr Ali Inname ne ya tabbatar da hakan, yana mai cewa lamarin ya faru a ƙauyen Bargaja da ke ƙaramar hukumar Isa a jihar Sokoto.

Kwamishin ya ce, iyalan sun ci wani sinadarin guba da ake kiran sa Gishirin Lalle, wanda suka yi amfani da shi a matsayin gishiri a abinci.

Dr Ali Inname ya ce, dukkanin iyalan da suka ci gubar sun rasa rayukan su, yayin da wasu biyu a ciki suka tsallake rijiya da baya sai dai suma suna karbar kulawar likitoci.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!