Labarai
Iyalan Nasir El-rufa’i sun koka bisa halin da ya ke ciki a hannun EFCC

Mataimaki na Musamman ga tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, kan harkokin yaɗa labarai, Muyiwa Adekeye, ya bayyana damuwa kan halin lafiyar ubangidansa yayin da yake tsare.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, Adekeye ya yi zargin cewa El-Rufai ya fuskanci matsalar zubar jini ta hanci a ranar 17 ga watan Fabrairun da muke ciki.
Ya ce an hana matarsa damar kai masa abinci kai tsaye, lamarin da ya kara dagula damuwar iyalansa da lauyoyinsa.
Sanarwar ta ce suna ci gaba da fuskantar ƙalubale wajen samun damar ganawa da shi, duk da cewa kwanaki takwas kenan da tsare shi.
A cewarsa, an tsare tsohon gwamnan ne tun bayan da ya miƙa kansa ga EFCC a ranar 16 ga Fabrairu 2026, sakamakon gayyatar da hukumar ta yi masa domin amsa wasu tambayoyi.
Har zuwa lokacin fitar da sanarwar, babu wata sanarwa a hukumance daga EFCC da ke mayar da martani kan zarge-zargen da mataimakin ya yi.
You must be logged in to post a comment Login