Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Addini

Iyaye su sanya idanu kan yaransu da ke kwana a shaguna – Ibn Sina

Published

on

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta bukaci al’umma musamman iyaye da su kara sanya idanu a kan yaran su, da suke kwanan shago ko waje a wannan lokaci na zafi don sanin me suke aikata.

Babban kwamandan hukumar Shiekh Harun Muhammad Sani Ibn Sina ne ya yi wannan kiran.

Ya ce, wannan ya biyo bayan samun wasu matasa biyu masu kwanan shago a unguwar Dorayi da laifin shigar da ‘yan mata shagon da su ke kwana kuma suna yin lalata da su.

“A yau abin takaici mun kama matasa da wasu ‘yan mata a shago wadanda dukkanin su iyayen su basu san suna aikata irin wannan laifin ba, domin kuwa ciki har da amaryar da ya rage saura watanni uku auren ta”.

Shiekh Muhammad Harun Ibn Sina ya kuma bukaci matasa da su sanya tsoron Allah a zukatan su don gujewa fadawa halaka.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!