Labarai
Jagororin PDP da ADC sun yi taron sirri a Abuja

Shugabannin jam’iyyun adawa na PDP da ADC sun gudanar da wani taron sirri a birnin Abuja, a gidan tsohon shugaban majalisar dattawa David Mark.
Rahotanni sun bayyana cewa taron ya samu halartar manyan jiga-jigan jam’iyyun biyu, inda suka tattauna muhimman batutuwan da suka shafi siyasar kasar nan da kuma lalibo hanyoyin da zasu kawo karshin jamiya mai mulki ta APC .
Majiyoyi sun ce ganawar na daga cikin kokarin da shugabannin jam’iyyun ke yi na ci gaba da tattaunawa tsakanin masu ruwa da tsaki, domin karfafa hadin kai a tsakanin su kafin manyan zabukan da ke tafe.
Sai dai har yanzu babu cikakken bayani abubuwan da aka tattauna a lokacin gudanar na wannan taro.
You must be logged in to post a comment Login