Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

ilimi

JAMB: An sake naɗa shugaban hukumar a karo na biyu

Published

on

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya sake naɗa Farfesa Ishaq Oloyede a matsayin shugaban hukumar shirya jarrabawar shiga manyan makarantun Ƙasar nan JAMB.

Wannan na cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ma’aikar ilimi ta ƙasa Ben Bem Goong ya fitar.

A cewar sanarwar, nadin nasa a karo na biyu ya biyo bayan yabawa da ministan ilimi Adamu Adamu yayi da salon shugabancin sa, wanda hakan zai bashi damar sake shafe tsawon shekara biyar yana jagorantar hukumar JAMB a karo na biyu.

Labarai masu alaƙa:

Yanzu-yanzu- JAMB ta saki sakamakon jarrabawar UTME ta bana

Kazalika shugaba Buhari ya sake naɗa Farfesa Abubakar Rasheed a matsayin shugaban hukumar kula da jami’o’i na ƙasa, da Hamid Bobboyi a matsayin shugaban hukumar kula da ilimin bai ɗaya ta ƙasa da sauran naɗe-naɗe.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!