Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

JAMB: ta kammala shirin fara sayar da form na 2021

Published

on

Hukumar shirya jarabawar JAMB, ta sanar da kammala shirye-shiryen siyar da form din jarrabawar tantance shiga manyan makarantun gaba da sakandire, na UTME da DE, na shekarar 2021/2022.

A wata sanarwa da hukumar ta fitar a mujallar ta, ta mako mako yau Litinin 15 ga watan Maris a Abuja, hukumar ta ce siyar da form din da kuma gudanar da jarrabawar ba zai wuce zuwa 24 ga watan Maris din da muke ciki.

Hukumar ta JAMB, ta ce tsaikon da aka samu na gudanar da jarrabawar a bana, ya samo asali ne saboda Annobar Corona, data tsayar da al’amurra da dama a fadin kasar nan da ma Duniya baki daya.

Hukumar ta kuma tabbatar da cewa za ta kammala shirye shirye akan lokaci don ganin ba a samu koma baya ko tsaiko da zai shafi dumbin daliban kasar nan dake da niyyar yin Jarrabawar a Bana.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!