Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

JAMB:ta kama mutane 50 wadanda suka kware wajen rubutawa dalibai jarabawa

Published

on

Hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantun gaba da Sakandire ta kasa JAMB, ta zargi wasu daga cikin jami’oi masu zaman kansu na kasar na da taimakawa ayyukan cin hanci da rashawa.

 

Shugaban hukumar ta JAMB Farfesa Is-haq Oloyede ne ya bayyana haka a wajen wani taron jami’oi masu zaman kansu da ke gudana a Abuja, wanda hukumar kula da jami’oi ta kasa ta shirya.

 

Ya ce shekarun baya gwamnati ta baiwa bangarorin masu zaman kansu da su sanya hannu a bangaren ilimi sai dai manufar shirin bai samu nasara ba sakamakon irin badakalar da ke faruwa.

 

Farfesa Is-haq Oloyede ya kuma ce halin da jami’oi masu zaman kansu ke ciki a kasar nan abin damuwa ne a don haka ya bukaci dukkannin masu ruwa da tsaki da rika aiki tare don ganin an magance matsalar.

 

Tun farko da ya ke gabatar da nasa jawabi shugaban hukumar kula da jami’oi ta kasa Farfesa Abubakar Rasheed, cewa ya yi, hukumar a yanzu haka ta karbi wasikar neman kafa sabbin jami’oi masu zaman kansu guda dari uku da uku.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!