Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Libiya ta dawo da yan Najeriya 136 filin jirgin saman jihar Lagos

Published

on

Hukumar bada agajin gaggawa ta kasa NEMA ta sake karbar ‘yan Najeriya 136 daga kasar dake zaune a kasar Libiya da suka yi carko-carko a can.

 

Jami’in dake kula da shiyyar Lagos Alhaji Idris Muhammed ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai da safiyar yau Talata.

 

Alhaji  Idris Muhammed ya kara da cewar ‘yan Najeriya sun sauka a filin jirgin saman Murtala Muhammed dake Lagos da misalin karfe 11 da minti 50 na daren jiya Litinin cikin jirgin saman Al-Burka mai lamba MJI.

 

A cewar babban jami’in an dawo da ‘yan gundun hijira ne tare da hadin gwiwar hukumar kula da bakin haure ta duniya da kungiyar tarayyar Turai tare tallafin shirin dawo da bakin haure na ‘yan sa kai AVR, wadanda suke taimakawa bakin haure dawo kasar su ta haihuwa.

 

Daga cikin wadanda aka dawo da su gida Najeriya akwai mata matasa 59 da jarirai 5 da kuma kananan yara 4.

 

Sauran su ne maza 63 da kananan yara 5.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!