Connect with us

Labarai

Jami’an Civil Defence sun cafke mutumin da ake zargi da satar kayayyakin makaranta

Published

on

Hukumar tsaron ta Civil Defence a jihar Jigawa, ta kama wani mutum da ake zargi da satar kayayyaki a wata makarantar sakandare da ke ƙaramar hukumar Dutse.

 

Mai magana da yawun hukumar a jihar, ASC Badruddeen Tijjani Muhamud, ne ya bayyana hakan cikin wani saƙo da ya aikowa Freedom Radio. 

 

Ya ce jami’an hukumar sun samu nasarar cafke wanda ake zargin ne bayan samun bayanan sirri da kuma gudanar da sintiri a yankin.

 

ASC Badruddeen Tijjani Muhamud ya ƙara da cewa hukumar za ta ci gaba da gudanar da cikakken bincike kan lamarin, kuma da zarar an kammala binciken za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu domin fuskantar hukunci.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!