Labarai
Jami’an KAROTA sun jikkata wasu matasa
Wasu jami’an hukumar kula da zurga-zurgar ababen hawa ta jihar Kano KAROTA, sun jikkata wasu matasa a nan Kano bayan da suka yi musu duka da gorori a bakin danjar Kantin kwari da tsakar ranar yau Lahadi.
Guda daga cikin wadanda yan KAROTAr suka yiwa dukan mai suna Surajo Sadiku Umar Warure da ya zo nan gidan rediyon Freedom jina-jina ya ce, yan karotar sun yi musu kwantan bauna ne suka kuma rufe su da duka.
Surajo Warure ya ce suna tura kayan sana’ar su ne bakin kasuwar kwari a kuraye, kwatsam yan karotar suka bayyana suka kuma kwace kayayyakin nasu, a cewar sa a kokarin suna bin bahasin kayan nasu ne suka rufar musu da duka da gorori.
Haka kuma ya sahida cewa akwai wani guda mai suna Inuwa Isyaku da shi ma jami’an Karotan suka yiwa dukan kawo wuka da a yanzu haka yana kwance a asibiti rai a hannun Allah.
Ko da muka tuntubi jami’in hulda da jama’a na hukumar ta KAROTA Nabulisi Abubakar Kofar Na’isa ya ce, ko da yake labarin bai isa gare su ba amma zai bincika da zarar ya kammala bincike zai sanar da mu.
Ko a jiya dai sai da aka samu wata danbarwa tsakanin jami’na KAROTAR da wani direban mota da suka yi sanadin mutuwar wani jami’in hukumar wasannin a nan jihar Kano bayan da suka take shi da mota.
Haka zalika a cikin abin da bai gaza kwanaki biyar ba direbobin manyan mota a nan Kano suka gudanar da wata zanga-zanga bayan da jami’an KAROTAn suka fasa wa wani direban mota kai saboda ya ce ba za su tuka masa mota ba.