Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Jami’an lafiya 141 ne suka kamu da Covid-19 a Kaduna

Published

on

Kwamitin yakin da cutar Corona na jihar Kaduna ya ce, ma’aikatan lafiya dari da Arba’in da daya ne suka kamu cutar Corona, tun daga watan Afrilu zuwa wata da muke ciki na Yuli.

Shugaban kwamitin Dr. Neyu Illiyasu ne ya tabbatar da hakan yayin zantawa da manema labarai a can Jihar ta Kaduna.

A cewar sa, lokaci ya yi da hukumomin lafiyar jihar, za su kara kaimi wajen ganin sun kare lafiyar ma’akatar jihar daga kamuwa ko yada cutar a tsakanin su.

Dr Neyu Illiyasu ya kuma ce, daga cikin wadanda suka kamu da cutar an samu ma’aikaci lafiya daya da ya rasa ransa sakamakon cutar, inda wadanda ke dauke da cutar a fadin Jihar sun kai kimanin dubu daya da goma sha shida.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!